Advert
Home Sashen Hausa Wani Sanata ya makale a hanyar Abuja saboda ambaliyar ruwan sama 

Wani Sanata ya makale a hanyar Abuja saboda ambaliyar ruwan sama 

Wasu sassan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja zuwa Okene sun kasance cikin ambaliya a ranar Asabar 7 ga watan Agusta wacce ta mamaye su bayan ruwan sama na awa hudu. Daya daga cikin yankunan da abin ya shafa shi ne tsakanin Kwali da Abaji.

Ambaliyar ta sa matafiya sun makale yayin da motoci daga Abuja ba za su iya wucewa zuwa Lokoja, Okene da sassan kudanci ba.

Kimanin motocin bas guda uku ne rahotanni suka ce ambaliyar ta kwashe su. Daga cikin daruruwan matafiya da suka makale har da Sanata daga gundumar Kogi ta yamma, Sanata Smart Adeyemi, inji rahoton The Nation.

Adeyemi ya ce: “Ambaliyar ta yi barna sosai. Na shaida yadda ta yi awon gaba da wasu motoci daga babbar hanya.

”Ni da matafiya da yawa ba za mu iya ci gaba da tafiya ba. Mun makale. Babu wata mafita da ta wuce komawa Abuja.”

Wata da cikin matafiya, Hadiza Abdulkareem ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su yi gargadi da fadakar da matafiya a wannan damina.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bada tallafin kudi dubu N200,000 ga kowanne ɗaya daga cikin iyalan mutum 18 da ambaliyar ruwa ta kashe a Doguwa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan ya kai ziyara ta musamman domin ta’aziyya ga iyalan mamatan ranar Lahadi.

Ya kuma yi addu’ar samun rahama ga waɗanda suka rasu sanadiyyar ruwan sama mai tsanani, wanda ya haifar da ambaliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: