Advert
Home Sashen Hausa Wani matashi a Katsina, ya kashe kansa bayan tsananin damuwa...

Wani matashi a Katsina, ya kashe kansa bayan tsananin damuwa…

Wani matashi a Katsina, ya kashe kansa bayan tsananin damuwa…

Rahotanni da Katsina City News ta samu ya tabbatar mana da Mutuwar yaron mai suna Nura dake Unguwar tudun ‘yanlifida a cikin garin katsina ta hanyar rataye kansa, a saman rufin dakin gidansu…

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta ta sheda mana, cewa suna zargin Matashin ya shiga damuwa ne wadda tayi dalilin rataye kansa, tun bayan da jami’an tsaron ‘yansanda suka nuna mahaifiyarsa a wani Faifan bidiyo, Inda ake zargin tana sayen man Fetur domin saidawa masu garkuwa da mutane a Daji,

Koda yake wani ɗan’uwa na jini daga cikin ‘yan’uwan mamacin ya shedawa wakilin mu cewa, yaron yanada lalurar tabin hankali,

Har wayau majiyar Katsina City News ta sheda mana cewa, Mahaifiyar Mariganyin Malama Umma, Mijinta ya mutu, tana da Marayu a gabanta da take dawainiya dasu, shine dalilin da yasa ta shiga wannan sana’a ta safarar man fetur zuwa garin magamar jibiya, amma sun sheda mana, a iya sanin su, matar bata da alaƙa da masu garkuwa da mutane, sai dai kawai tana kai manfetur din ne Magama, duba da yanda ake ƙarancin Fetur din acan.

“Nura yaro ne mai natsuwa, wanda kusan yana kular mun da komai na kasuwanci na, amma lokacin da aka kama mahaifiyarsa ya shiga damuwa har wata rana, yazo gidana yace akwai wani wanda zai taimaka masa don mahaifiyarsa ta fito, nace yayi hakuri tunda ga hanyar da ake bi, muga abinda hali yayi, tun daga nan ya kama surutai, yace, lallai sai na kasheshi, daga nan na fahimci baya cikin hayyacinsa.

Ranar da zai rataye kansa, yana shago sai, naga ya tashi ba lokacin da ya saba tashi ba, kuma har yana hawaye, sai na fahimci matsalar da yake fama da itace ta taso, shine nasa aka daukeshi aka kaishi gida, tsakar dare sai aka cemani ai ga abinda Nura yayi” inji dan’uwan mamacin.

Katsina City News ta jiyo mahaifiyar yaron data samu iskar ‘yanci daga hannun jami’an tsaro tun gabanin yaron ya kashe kansa, tana cewa yaron ya shiga damuwa ko bacci bayayi, wani lokaci ma sai ya kama kuka, (hawaye) to amma dai muna lallashin sa gami da addu’a, harda magunguna saboda muna zaton, ko yasamu tabin hankali,

A ranar da zai kashe kansa da daddare, naga ya ƙi shiga daƙi ya kwanta. Ya zauna waje yana kuka, sai na lallaɓashi na bashi fitila yaje daki (inda yake kwana) ya kwanta, amma dukda haka ban natsu ba, sai na kasa bacci, na tashi na shiga dakin nasa inga ya yake, sai naga fitilar wayar da na bashi, kunne amma baya bisa shinfidar sa, induba sai naga yaro ya rataye kansa, anan na nemi taimakon jama’a gami da jami’an tsaro, aka kaishi asibiti aka tabbatar mana da ya mutu.

Idan ba’a manta ba a watan da ya shuɗe ne, Rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina ta nuna Mahaifiyar yaron a wani faifan bidiyo tare da wasu mata biyu da ake zargi da keta Doka, ta hanyar sayen Fetur daga nan cikin garin Katsina zuwa Jibiya.

 

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...