Wani mai Mota ya daki motar sarkin Kano Aminu Ado Bayero a tsakiyar birnin Kano.

Labari Daga jihar Kano na cewa Sarkin Kano Aminu Ado yayi hatsarin mota a Kano, har direba sa ya ji rauni.

Kakakin rundunar Ƴan sandan Kano Abdullahi Kiyawa ya sanar da hatsarin mota da sarkin Kano Aminu Ado Bayero yayi a cikin garin Kano.

Haruna-Kiyawa ya bayyana cewa ” Daya daga cikin motocin dake tare da Sarki Aminu ne ya gogi wata mota kirar Toyota a Gadar Lado. Nan take ya garzaya da direban motan zuwa asibitin Murtala domin a duba shi.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta karyata labaran da ake yadawa wai an kai wa sarki Aminu hari don a kashe shi ne.

Sai dai wasu na zargin kamar da nufi aka dirkaki motar sarkin.

Allah ya kiyaye na gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here