Wani Magidanci ya rataye kansa a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Wani magidanci ya rataye kansa da kansa a unguwar Sauna Kawaji da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano,

Magidancin Mai suna Sabi’u Alhassan mai shekaru 62, an samu gawarsa ne a gidansa bayan matarsa ta fita unguwa,

Shaidun gani da ido sun shaidawa Jaridar Taskar Labarai cewa, su ma ba su san dalilin da ya sa wannan dattijo ya aikata wannan aika aika ba,

Duk da ya ke cewa babu tabbacin shi ne ya kashe kansa, amma hukumar yan sanda na jihar Kano sun fara binciken musabbabin wannan aika aika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here