Barayin Daji sun kai hari jiya Litinin 28/06/2021 a garin Funtua dai dai lokacin da ake gudanar da Sallah Isha’i a daren Jiya Inda sukayi awon gaba da wata Mata mai Ciki kimanin Watanni Takwas da wani Yaro.

Mutanen Unguwar sun bayyana cewa Barayin sunzo ɗauke da Bindigogi suka fara harbi saman Iska wanda yasa Mutane ranta a na kare Sallah ma bata kammala ba, Barayin sun shiga Gidan da wannan baiwar Allah take inda suka tasata gaba suka tafi da ita.

Bayan da aka kira Maigidanta aka sanar dashi halin da ake ciki nan take ya dawo gida ya tambayi Inda ake sa ran Barayin sunbi domin yabi bayan su, Mutane sunyi yunkurin hanashi amma yace bazai bari atafi da Matar shi ba kawai ya zauna yana zaman jiran tsammani.

Bayan ya sanar da Jami’an tsaron Ƴan Sanda, inda suka tabbatar mashi da cewa sun san da lamarin kuma Jami’an su na wurin, Maigidan wannan Mata ya bayyana mana cewa yabi hanyar ƙauyen Maigandi Inda yake sa ran nan Barayin suka bi, amma a rashin sani Barayin sunbi Arewaci ne ta wata Unguwa mai suna Ungududu, bayan yayi nema ya gaji ya dawo gida inda suka cigaba da Adduo’in neman tsari.

Allah cikin Ikon shi Barayin dole suka barta a wajen Mahuta saboda tayi Nauyi bata iya tafiya sakamakon ciki da take dashi, Ƴan Sa-kai a Mahuta ne suka yi cin karo da ita Inda suka rako ta Gida wajen ƙarfe Goma Sha Daya da rabi na Dare.

Hakan yana faruwa ne ƙwana biyar bayan Barayin sunzo garin sun sace Mutane wadanda har yanzu suna hannun su, wannan Matar ta bayyana ma Maigidan ta cewa Barayin sun gaya mata ta sanar dashi cewa zasu dawo.

Mai Gidan yayi kira ga Al-umma cewa ya kamata fah Mutane su daina tsoro koyaya a riƙa nuna tirjiya domin kare kai daga wadannan Miyagun, hakan nan yayi kira ga Jami’an tsaro dasu ƙara kaimi wajen bada tsaro ga Al-umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here