Wani alkali a Kano ya umarci Ganduje ya biya Jaafar Jaafar kudin da kotu tace a bashi

Alkali babbar ko a jihar Kano, Sulaiman Baba Namalam, ya umarci Gwamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da ya biya Jaafar Jaafar kudin da kotu ta umarta da a biya shi a Shariar da shi Gandujen yakai Jaafar, kuma daga bisani ya janye karar.

Babbar Kotun Kano dai ta umarci Gwamna Ganduje da ya biya mawallafin jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar zunzurutun kudi Naira dubu dari takwas, ladan bata masa lokacin da Gwamnan yayi a karar da ya kai Jaafar din daga bisani kuma ya janye karar.

Har yanzu dai Gwamnan bai biya mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar kudin da kotu ta umarta a biya shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here