Tsohon Kwamishinan Noma, kuma mataimakin Gwamnan jihar Katsina Qs. Mannir Yakubu ya kaddamar da fitowa takarar sa a Babban Ofishin Jam’iyyar APC na jihar Katsina.

Qs. Mannir Yakubu shine mataimakin Gwamnan Katsina Aminu Masari, na tsawon shekaru bakwai a Ranar Litanin 25 ga watan Fabrairu ya fito da masoyansa zuwa ofishin Jam’iyyar APC domin bayyana ma shuwagabannin Jam’iyya aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Katsina a shekarar 2023.

Da yake jawabi a wajen taron QS. Mannir Yakubu ya fara zayyano irin gagarumin ci gaba da Gwamnatin Aminu Masari ta kawo ma jihar Katsina tun hawan Mulkin su a shekarar dubu biyu da sha biyar zuwa yanzu, sana ya kara bayyana irin ci gaban da ya kawo a karkashin Ofishin sa na Kwamishinan Noma, a karshe Qs ya bayyana ra’ayinsa na shiga sahun ‘yan takarar da zasu fafata a zaben fidda gwani da zai gudana a wata mai kamawa.

Taron wanda ya hada dukkanin shuwagabannin Jam’iyyar APC na jiha da na ƙaramar Hukumar Katsina tsaffin kwamishinoni mashawartan gwamnati, (S.A) da sauran su.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina ya yaba da ƙoƙari da irin hakuri na Mataimakin Gwamnan Katsina kuma yace lallai mutum ne nagartacce. Bala Abu Musawa shine mataimakin Jam’iyyar APC na jiha yayi karin haske da jinjina ga Gwamnatin jihar Katsina da shi kansa mataimakin Gwamnan inda yace wasu ‘Yantakarar, saura kwanika a yi zaben fidda gwani amma basu da Lafiya ta neman magani suke, amma QS Mannir Yakubu nagartacce ne mai lafiyar da zai iya jagoranci.

Daga nan ofishin Jam’iyya QS. Mannir Yakubu ya ja tawagarsa zuwa cikin garin Katsina domin sanarwa masoya yan’uwa da abokan arziki cewa, ya fito Takarar Gwamnan jihar Katsina.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here