Abdullahi Umar Ganduje: Shin wane ne ya wanki Gwamnan jihar Kano?

Jami’ar ta ce babu wata magana mai kama da haka tsakaninta da Ganduje, kuma takardar da wani ma’aikacinta ya aike wa gwamnan ba ta samu amincewar mahukuntar jami’ar ba.

Batun bai wa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje matsayin farfesa a jami’ar East Carolina ta Amurka na ci gaba da ta da ƙura a Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta.

Mafi yawa masu tsokaci na yin tambaya ne iri ɗaya kan wane ne ya bai wa Ganduje wannan matsayi, tun da jami’ar da aka alaƙanta da ba da matsayin ta musanta yin hakan.

Jami’ar ta ce babu wata magana mai kama da haka tsakaninta da Ganduje, kuma takardar da wani ma’aikacinta ya aike wa gwamnan ba ta samu amincewar mahukuntar jami’ar ba.

Wannan abu ya fusata gwamnatin Kano da shi kansa Gwamna Ganduje, abin da ya sanya suka nemi jami’ar ta bayar da haƙuri sannan a hukunta malamin jami’ar da ya bayar muƙamin “wanda ya yi yunƙurin kunyata gwamnan.”

Tun da farko sakataren watsa labarai na jihar Kano, Abba Anwar ne ya fitar da wata sanarwa da ke cewa Jami’ar East Carolina a Amurka ta ba Ganduje matsayin Farfesa sakamakon abin da ta kira “ƙwarewarsa wurin gudanar da mulki na gari da kuma inganta rayuwar al’umma”.

Kuma a cewar sanarwar, aikin Farfesan na gwamnan ya shafi bayar da shawarwari ga ɗalibai masu digiri na uku, da kuma ƙananan malamai.

Daga baya dai an gano wani mutum mai suna Victor Mbarika ne ya aika wa Ganduje wannan wasiƙa da jami’a East Carolina ta Amurka ta ce ba ta san da ita ba.

WANENE VICTOR MBARIKA?

Victor Mbarika wani farfesa ne a Amurka ɗan asalin ƙasar Kamaru, kuma yana koyar da harkar sadarwar zamani a cibiyar sadarwa ta jami’ar East Carolina.

Daga 2004 zuwa 2020 ya koyar da irin wannan darasi amma a jami’ar Southern Carolina.

A wata maƙala da Farfesa Farooq Kperogi, ɗan Najeriya da ke koyarwa a wata jami’ar Amurka ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce Victor Mbarika shi ke jagorantar duka cibiyoyin biyu.

Farooq Kperogi ya bayyana wasu abubuwa da Victor Mbarika ya yi amfani da su a wasiƙar da ya aike wa Ganduje waɗanda ya ce ba haka ake amfani da su a jami’a ba, musamman jami’o’in Amurka.

Kperogi, wanda ya shafe kusan shekara 20 yana cikin harkokin jami’a a Amurka, ya ce an yi manyan kura-kurai a turancin da aka rubutu ban da kuma ainihin yaren da aka riƙa amfani da shi ba daidai ba a wasiƙar wanda ya kamata ya alamta cewa ba ta gaskiya ba ce, tun kan gwamnatin Kano ta fitar da sanarwa kan batun.

Ya kuma taɓa kawo wata wasiƙa makamanciyar ta Ganduje a kan tsohon mataimakin shugaban majalisar datawan Najeriya Ike Ekweremadu a baya.

Victor ne ya ba shi matsayin farfesa, kuma malamin jami’a da zai riƙa zuwa yana koyarwa lokaci zuwa lokaci a jami’ar Southern Carolina, a lokacin Victor Mbarika na jami’ar.

An yi amfani da salon magana iri ɗaya cikin wasikar da aka aika wa Ganduje da wadda aka aika wa Ekweremadu a wancan lokacin, kuma duka Victor Mbarika ne ya aike da su, saboda shi ne ke jagorantar cibiyar ICT ta duka jami’o’in.

Shin akan su Ganduje aka fara?

Bayar da matsayin (Farfesa) ko (Dakta) ga manyan mutane ko ‘yan siyasa a Najeriya daga wasu jami’o’in ƙasashen waje ba sabon abu ba ne.

Amma na wankiya irin wanda wasu suke ganin an yi wa Ganduje da Ike Ekweremadu bai fito ba sosai sai a wannan lokacin.

Da wannan rikici da ya ɓarke tsakanin Ganduje da jami’ar East Carolina ta Amurka, masu matsayi da kuma ‘yan siyasa za su riƙa sanya alama tambaya ga irin waɗannan matsayi da za a riƙa ba su anan gaba.

Rahoton BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here