Advert
Home City News Wanene Sanata Abubakar Sadiq Yar'Adua...?

Wanene Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua…?

Wanene Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua…?

….Tarihinsa, Aikace-aikacensa, Siyasarsa

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Sanata Abubakar Sadiq Yar’Adua, Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin Jam’iyyar APC

Tarihin Sanata Abubakar Sadiq ‘Yar’adua.

An haifi Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua a ranar 6 ga Yulin shekarar 1960. Ya yi Makarantar Firamare a ‘Gidado Primary School’ da ke Rafukka Katsina.

Da ya kammala firamare dinsa, sai ya wuce Makaranta ta gaba (Sakandare) inda ya shiga Makarantar ‘Emergency Teachers College’ da ke Daura. Bayan ya kammalata, kaitsaye sai ya wuce Jami’ar Bayero (BUK) a shekarar 1981 zuwa 1985, inda ya yi digirinsa na farko a kan B.A Mass Communication, a yayin da ya kasance daya daga cikin mutane 4 da suka yi zarra a Department dinsu a shekarar.

A shekarar ta 1985, bai tsaya ba, sai ya sake komawa jami’ar ta Bayero inda ya yi Digiri na biyu (Masters) a kan harkokin Kasuwanci ‘Business Administration’.

A shekarar 1986, Sadiq ‘Yar’dua ya shiga jami’ar Legas inda ya kara yin wani digirin a kan kimiyyar Siyasa ( Political Science), digirin da ya fita da sakamako mafi daraja (first class)

Haka nan kuma, a shekarar 2016 Sanata Sadiq ‘yar’dua ya shiga jami’ar Success da ke kasar Ingila, inda ya kara yin wani Digirin a kan harkokin kasa da kasa (International Relations)

Yanzu haka kuma, Sanatan yana dalibta a jami’ar birnin Haol da ke Ingila, inda yake karatun dakta a ɓangaren Shari’a.

A ɓangaren aikin gwamnati kuwa, Sanata Sadiq ‘Yar’adua ya fara da koyarwa (Teaching) a makarantar ‘Sada Primary School’ da ke karamar hukumar Kankia. Daga nan ya dawo cikin birnin Katsina, inda ya ci gaba da koyarwa a Makarantar ‘Farin Yaro Primary School’ makarantar da har sai da ya kai matakin mataimakin shugaban makarantar.

Daga nan kuma, ya koma ‘Garama Primary School’ da koyarwa, sannan ya tashi ya koma garin ‘Bakiyawa Primary School’ da koyarwar.

Bugu da kari, Sanata Sadiq Yar’adua ya yi aiki a ma’aikatar kudi ta tsohuwar jihar Kaduna a karkashin ofishoshin biya na Daura Da Katsina.

Bai tsaya a nan ba, Sanatan ya yi ayyuka da dama, inda a ɓangaren aikin Jarida (da ya fara yin digiri a kansa) ya yi aiki da jaridar ‘Today’ a matsayin dan rahoto, inda har ma ya zama editanta na yanki a lokacin Mulkin Ibrahim Badasi Babangida. Har wayau ya zama editan jaridar na jihar Legas da kewaye, sannan ya kara zama editan jaridar baki daya a jihar Kaduna.

Bayan nan kuma ya yi aiki da gidan rediyon BBC a sashe biyu; turanci da Hausa.

A lokacin da yake aiki da rediyon BBC lokacin yakin Laberiya, gwamnatin jihar Katsina karkashin John Yahaya Madaki ta nada shi a matsayin babban jami’i mai magana da yawun Gwamna.

An kuma sake mai da shi a wannan mukami da mai magana da yawun gwamna a lokacin Gwamnatin Sa’idu Barda.

Bayan nan ya koma Legas inda ya yi aiki a matsayin jami’i mai kula da hada-hadar shigowa da jiragen ruwa a karkashi NIMASA. Daga nan kuma Obasanjo ya nada shi babban darakta a karkashin Kamfanin nan mai kula da tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya.

Haka nan kuma a shekarar 1999 zuwa 2023, Sanatan ya yi dan majalissar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Katsina a Majalissar wakilai ta Kasa. Ya kuma zama shugaban ma’aikatan ofishin kakakin majalissar wakilai ta kasa a lokacin da Aminu Bello Masari ke kakakinta a shekarar 2013 zuwa 2007.

Haka kuma Sanatan ya wakilci shiyyar Katsina a Majalissar dattawa a shekarar 2011 zuwa 2012.

Sanatan bai tsaya nan ba, ya kuma yi muhimman ayyukan ci gaba a ciki da wajen jihar Katsina, Musamman a jihar katsina inda ya yi ayyuka da dama na taimakon al’umma da suka hada da taimakon gajiyayyu da marasa karfi, Mata da Yara da kuma  Matasa.

Yanzu kuma, Sanata Sadiq ‘Yar’adua ya fito takarar gwamnan jihar Katsina karkashin jam’iyyar All Prograsive Congress APC.

“Kowa yasan ƙasarnan ana zalunci, Jihar mu ta Katsina ana Zalunci, kowa ya sani. To ni na fito Takarar Gwamnan jihar Katsina ne domin inyi yaƙi da zalunci da wawure Dukiyar Al’uma da ake a jiha kuma nayi Al’ƙawarin yin haka, idan na zama Gwamna” wannan wasu daga cikin Maganganun da Sanata Sadiq Yar’Adua ke yawan nanatawa ga al’uma a duk lokacin da yaje taronko aka zo masa domin goyon bayan.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

KUDENDAN POWER STATION AND MANDO SUBSTATION PROJECT REACHED FINAL STAGE OF COMPLETION #PositivefactsNG

The federal government is working tirelessly to complete Kudendan power station and Mando substation in Kaduna state, the state minister of power Engr. Sale...

MATSALOLIN TSARO: Gwamnatin Zamfara tabawa duk dan jiharta damar Mallakar Bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Bai Wa Ƴan Jihar Damar Mallakar Bindiga don kare kansu daga harin ƴan bindiga Gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin...

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...
%d bloggers like this: