Wanene Mai Shari’a Adamu Bello sabon Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kankara?

Mai Shari’a Alh. Adamu Bello, Shima yana ɗaya daga cikin Zuri’ar Iya Nadabo, wanda Shine ke Shugabantar Zuri’ar.

Ɗa ne ga Marigayi Sabon Gari Alh. Muhammad Bello Ɗan Sarkin Pauwa Nuhu, Ɗan Iya Abdullahi Nadabo, Ɗan Waziri Usman Kosau, kuma Surukin Late Chiroma Alh.Yakubu Nadabo Pioneer Chairman na Zuri’ar Iya Nadabo Family Association.

Tsohon Ɗalibin Government College Funtua, Ahmadu Bello University, Zaria. Yayi aiki a gurare da dama, da suka haɗa da Ministry of Health Kaduna State, kafin a ƙirkiri Katsina State.

Alƙalin Magistrate Court Funtua, Dutsinma, Ag. Chief Registrar Katsina State High Court, Judge Federal High Court Lagos, Federal High Court Kwara, Federal High Court Ibadan, Federal High Court Porthacourt, Federal High Court Kano, Sokoto, da Federal High Court Abuja inda yayi ritaya ya kammala Wa’adin Aikin shi.

Daga bisani Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari yazabeshi, inda yabashi Permanent Board Member na ICPC saboda gaskiyarshi, rikon amana da kishin ƙasa wanda yakeyi har kawo yanzu…

Allah ya taya riƙo ya tabbatar da Alkhairi yabada ikon kawo sauyi mai Ma’ana da zaman Lafiya mai dorewa a yankin Ƙanƙara dama jihar Katsina baki Ɗaya Amin

Hausa7 TV ta dakko labarin daga shafin marubuci Muhammad Aminu Kabir

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here