WANENE KASIMU NAGARI
Cikakken Sunansa shi ne Kasim Ibrahim Nagari.

An haifi Alh. Kasimu Nagari a garin Kunduru da ke karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina a ranar Ashirin ga watan Agusta a shekarar 1962, (20th, August, 1962).

Alh. Kasim Ibrahim Nagari ya Shiga makarantar Firaimare da ke garin Radda daga shekarar 1968 zuwa 1975.

Daga nan kuma ya wuce zuwa Government College Katsina daga shekarar 1977 zuwa 1982, inda ya zama shugaban Dalibai wato (Head boy).

A Shekarar 1982 Alh. Kasim Ibrahim Nagari bai tsaya ba sai ya wuce makarantar College of Advanced Studies Zariya inda ya kammala a shekarar 1984.

Alh. Kasim Ibrahim Nagari ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello University da ke Zariya inda ya karanta Fannin Ilimin Kimiyyar Siyasa wato (Political Science), inda ya kammala a shekarar 1987.

Alh. Kasim Ibrahim Nagari ya yi hidima ga kasarsa wato (NYSC) a makarantar Sakandare da ke Yelwa Yawuri ta jihar Sokoto wacce a yanzu ta ke cikin jihar Kebbi, inda ya kammala a shekarar 1988.

Bugu da kari Alh. Kasim Ibrahim Nagari ya yi digirinsa na biyu wato (Masters) a Fannin (International Affairs and Diplomacy) a shekarar 2009.

Alh. Kasim Ibrahim Nagari ya yi aiki a zauren Majalissar Dokoki ta jihar Katsina wato (Katsina state house of Assembly) daga shekarar 1989 zuwa 1994.

Haka nan kuma ya yi aiki a Ofishin Gwamna daga shekarar 1994 zuwa wasu shekaru.

Alh. Kasim Ibrahim Nagari ya rike mukamai, kuma ya yi aiki da mutane daban-daban, sannan kuma ya halarci taruka da kwasa-kwasai a jihar Katsina cikin gida Najeriya har ma da kasashen ketare.

Alh. Kasim Nagari ya Jagoranci Kwamitoci da dama da aka nadashi ya shugabancesu ya zama mamba a wasu kwamitocin kuma ya cimma Dumbin Nasarori kan aikinsa.

Daya daga cikin Kwamitocin da ya Jagoranta a baya-bayan nan mafi Shahara da ya kara daukaka Darajarsa shi ne ya jagoranci Sakataren Kwamitin #S_POWER na jihar Katsina Wanda ke karkashin kulawar Ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammad Inuwa.

Alh. Kasim Ibrahim Nagari ya zama Babban Darakta a Political and Common services a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.

A halin Yanzu dai Alh. Kasim Ibrahim Nagari shi ne Babban Sakataren din-din-din wato Permanent Secretary a fannin (Political and Common Services Affairs) a ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Katsina.

A cikin wannan shekarar ta 2021 shugaban ma’aikata na jihar Katsina Alh. Idris Usman Tune ya mika masa lambar girmamawa da ta bayyanashi a cikin fitattu Kuma Jajirtacce tare da gogewa kan aiki a fadin jihar Katsina.

Wani abin lura dangane da rayuwarsa shi ne shi mutum ne mai Hakuri, saukin Kai, son mutane, sakin fuska da kuma Jajircewa akan aikinsa na gwamnati.

Allah ya albarkaci Alh. Kasim Nagari da mata biyu da ‘ya’ya goma sha biyu (12).

Fatanmu a nan Allah ya albarkaci zuri’a ya Kuma sa a gama aiki Lami lafiya.

Janaidu Amadu Doro, mai taimaka wa na musamman kan harkokin kafar sadarwar zamani a ofishin PS.

08 – 07 – 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here