WANE NE JANAR HASSAN USMAN KATSINA (CIROMAN KATSINA)?

WANE NE JANAR HASSAN USMAN KATSINA (CIROMAN KATSINA)?

An haifi Hassan a ranar 31 ga watan Maris a shekarar 1933. An haife shi ne a gidan mahaifinsa Sarki Sir Usman Nagogo shi da abokin haihuwarsa Hussaini (Naini). Sunan mahaifiyarsu fatima, an fi kiran ta da suna Cima ko Hajiya Uwargida ‘yar Wazirin Katsina, Haruna.

Hassan yana kasa da shekara shida aka kai shi gidan Kankiya Nuhu wanda kane ne a wajen kakansa, marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Kamar yadda kowane yaro yake tasowa a kasar Hausa, Hassan ya yi karatun Allo. Ya yi karatu a makarantar Elemantare ta Kankiya daga 1940-1943, ya wuce Midil ta Katsina daga 1944-1947. Daga nan ya wuce Kwalejin Barewa ta Zariya, daga 1948-1951. Hassan ya yi karatu a Institute of Administration da ke Zariya a 1952, ya wuce Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Nijeriya watau ‘Nigerian College of Arts, Science and Technology, Zariya a 1953-1955.

“Wata rana na zo wucewa wajen cin abinci sai na ga an manna takarda ta neman ‘yan Arewa masu son tafiya soja. Sai na ce ina so; ni dai kurum na ji ina so ba da wani na yi shawara ba, na yi kokarin bin ka’idar shigar ne. Amma ban fada ba don ba na son tsohuwata ta ji. Idan ta ji ba za ta yarda ba. Da aka yi hutu na koma gida sai na sanarwa da mahaifina Sarki cewa ina sa ran takarda ta neman tafiyar makarantar horar da hafsoshin soja. Sai ya ce, ka fada wa Hajiya?’ Na ce ‘a’a ban fada mata ba’, Sai ya ce to kar ka fada mata”.

Da zan komo Kaduna sai ya ba ni takarda na kai wa Wazirin Katsina, Alhaji Isa Kaita. Na zo Kaduna na yi jarrabawa, bayan mun kare na koma gida ina sauraren sakamakon jarrabawa. Ba zan taba mantawa ba, ana zaune wajen Hawan Daba don tarbar Sarauniyar Ingila sai na sami telegiram mai cewa na ci jarrabawa ana nema na a Kaduna.

“Na fada wa mahaifina. Muka kintsa muka bar Katsina sai Kaduna, daga Kaduna muka tafi Legas. Da isa ta Legas sai na ga abokan nawa da suka sami nasarar wannan tafiya duk ‘yan Kudu ne. Ni kadai ne dan Arewa kuma Bahaushe cikin mu takwas.

“Daga nan sai kasar Ghana, watau a shekarar 1957. Muka fara koyon aikin soja a Makarantar Horar da Hafsoshin Soja da ke Teshie ta kasar Ghana. (The Regular Officers Training School, Teshie Ghana).”

“A watan Nuwamba muka koma Ghana cikin jirgin sama, muka kwana a Gambiya, muka tashi sai tsibirin Sipanish. Kwananmu daya sai jabirota kwananmu biyu, duk cikin jirgin soja na B. Bush hakan ya faru ne a 1951. Na tafi wata makaranta ta koyon harbi da ke Ingila watau Mons Officers Cadet Aldershot, na je makarantar sojan kasa watau Royal Military Acedemy Sandhust Camberly England. Da na dawo gida sai aka tura ni Kawo, bataliya ta biyu ina nan wurin aka bude N.D.A. Lokacin ba haka sunanta yake ba Sunanta N.M.T.C.

“Ana nan sai Ministan Tsaro Muhammadu Ribado ya sa na zagaye duk makarantu ina lacca domin yara su shiga aikin soja saboda gaba. Daga nan ne muka samu su Abba Kyari da Murtala Muhammed, Hamza Abdullah Muhammadu Bahari, suka shiga aikin soja”, kamar yadda Hassan Katsina ya bayyana.

Bayan an yi sallar magariba an sha ruwa, sai Hassan ya fada wa matarsa cewa zai tafi don ya gaisa da Sardauna kamar yadda ya saba, saboda lokacin azumi ne, kuma Sardauna ya dawo daga Umra tare da mahaifinta ita Hajiya Asiya, watau Alhaji Bello Bindawa. Bayan sun tafi ya kai ta gidansu ya wuce wajen Sardauna ya gaishe shi, ya wuce wajen Ademulegun. Nan ya dade suna hira. Bayan ya kare shirinsa ya koma ya dauki matarsa zuwa gida da misalin sha daya na dare.

Wazirin Katsina Isa Kaita shi ne ya sanar da Hassan, halin da ake ciki. Isa Kaita ya shi da masa cewar soja suna ta harbi da gidan Sardauna. Sai Hassan ya tambayi Waziri soja dai ko ‘yan bindiga? Bayan Hassan ya kare magana da Waziri, sai ya shir ya ya fita. Asiya matar Hassan, tace san da na buga waya ofishin Hassan ba zan manta ba Janar Babangida, lokacin yana Laftanar shi ne ya dauka. Na ce “Wa ke magana? Sai ya ce ‘Ni ne Ibrahim’. Sai na ce masa, ‘Ina maigidana?’ Sai ya ce, ga shi can tare da Chukuma, a kira shi?’ Sai na ce, ‘A’a. Ashe a wannan lokacin Chukuma ya tsare Ciroma.

“Da ya tsare Hassan da bindiga yana tambayarsa, shi kuma Hassan sai tambayarsa yake yi, ‘Ya na gan ka da raunuka Kaduna?’ Sai ya ce, ai mun kashe Sardauna mun kashe Ademulegun, an kashe Shodende. A takaice dai mu ke da mulki. Ya kara da cewa kai kana da ‘ya’ya biyu ni kuwa haka nake ba ni da kowa a nan Nijiriya, kana tare da mu, mu kyale ka ko kuwa ba ka tare da mu? Ya cullo masa karamar bindiga.

Olusegum Obasanjo shi ne Ironsi ya turo shi da takarda zuwa ga Hassan wadda a cikinta Ironsi ya nuna ya nada shi ya rike mukamin Gwamna na Jihar Arewa”.

Bayan da Hassan ya karbi wannan takarda nadinsa Gwamna, sai nan take ya sanar da mahaifinsa Sarki Usman Nagogo wanda ya ba shi goyon baya. A gwamnatin Gowon, ya rike babban hafsan Sojojin, kasa ta Najeriya, Hassan, ya ta ka mahimmiyar rawa a lokacin yakin basasan Nijeriya. Hassan shi ne Ciroman Katsina.

Allah ya karbi ran Hassan, ranar Litinin 24 ga watan Yuli a 1995. Allah ya yi masa Rahma.

Littafin da ya taimaka mana wurin bincike shi ne Gaskiya Nagartar Namiji Na Badamasi Shu’aibu Burji.

Rubutawa Abdullahi Musa Badayi

Daga Kasar Zazzau Jiya Da yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here