Advert
Home Sashen Hausa WAKE AIKI A KANKARA, SANATA YAKUBU LADO KO GWAMNATIN TARAYYA?

WAKE AIKI A KANKARA, SANATA YAKUBU LADO KO GWAMNATIN TARAYYA?

 

Muazu Hassan @Katsina City News

A satin da muke ciki hotuna da bidiyo suka cika shafukan sada zumunta na yanar gizo akan wani aikin hanyoyin cikin garin Kankara da akeyi.

Wasu jaridun yanar gizo ciki har da katsina city news sun dauki hotunan suka buga a matsayin wani aikin Alheri da wani Dan siyasa keyi ma al ummarsa kyauta.

Labarin ya jawo hankali da motsa jijiyar wuya, bayan da jaridar katsina city news ta buga hotunan.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mashi da Dutsi Alhaji Mansir Ali mashi ya bayyana ma daya daga cikin editocin jaridar cewa wannan aikin da Yakubu lado keyi na gwamnatin tarayya ne

Kuma an saka shi a cikin kasafin kudin 2021.Dan majalisar ya nuna ma editan takardun kasafin kudin na 2021.

Inda a ciki aka Sanya aikin hanya a Kankara jahar katsina kan kudin naira milyan dari biyu da tamanin.

Wannan aikin shine Wanda sanata Yakubu lado ya samo a matsayin dan kwangila daga gwamnan tarayya amma yake son ya karkatar dasu inji Alhaji Mansir ali mashi a matsayin aikin shi.

Dan majalisar ya kuma bankado wani aikin gwamnatin tarayya na naira milyan dari biyu da za a Gina dakunan kwana a wata makaranta mai zaman kanta ta horon aikin jinya.mai suna health technology Kankara.

A takardun da editan Katsina City News ya gani an saka naira milyan dari biyu a wannan makarantar da ba ta gwamnatin Jaha, Tarayyar ko Karamar hukuma ba.

Binciken Katsina City News ya gano makarantar ta wasu mutane ce kuma ko cikakken lasisi basu Samu ba.

Amma sun fara karatu da wani gidan da suke haya mallakin sanata Yakubu lado. Sannan sun saka sanata Yakubu lado a matsayin daraktocin makarantar.

Kwatsam sai ga sunanta kasafin kudin gwamnatin tarayya za a yi mata aiki na naira milyan dari biyu.

Shima wannan aikin Dan majalisar tarayya Alhaji mansur Ali mashi ya rubuta koken a dakatar dashi, a maimakon a gina ma wata makaranta mai zaman kanta aikin naira milyan dari biyu gara ayi wani aikin cigaba da kudin a karamar hukumar Kankara.

Wasu na zargin hatta ayyukan da akayi a garin Dan marke duk ta irin wannan hanyar akayi aikin.

Katsina City News ta gano an saka aiki kusan na bilyan daya a karamar hukumar Kankara a kasafin kudin 2021.

Daga cikin su akwai wata cibiyar koyon sana oi ta matasa.da wasu fitulu masu amfani da hasken Rana a wasu garuruwan Kankara.

Amma duk ayyukan nan yan majalisar tarayya na Kankara da sanatan yankin Kankara bai san da su ba.wanda ake zargin kamar wata karkatar da kudi ake son yi da wayon aiki.

Katsina city news mun tuntubi sanata Yakubu lado Dan marke don jin ta bakin shi bamu samu amsa ba. Mun aika masa sako ta whatssApp shima muna jiran amsa.

Katsina City News

Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

Www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

Www.thelinksnews.com

07043777779, 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: