Advert
Home Sashen Hausa Wajibi ne Gwamnati tabi kadin lamarin domin nemawa al'uma haƙƙinsu -Gwamna Masari...

Wajibi ne Gwamnati tabi kadin lamarin domin nemawa al’uma haƙƙinsu -Gwamna Masari ga mutanen Jibiya

Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki kwararru masana Shari’a da za su hadu da jami’an Ma’aikatar Shari’a domin zurfafa bincike a kan gangancin da jami’an kwastam sukayi wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka a garin jibiya. Za ayi wannan bincike domin tabbatar da anyi shirin da ya kamata domin gurfanar da hukumar a gaban kuliya idan har bata biya kudin diyyar rayukan da aka rasa ba.

Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi haka yau a garin Jibiya, yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya, tausayawa da kuma jajantawa ga al’ummar garin, musamman wadanda abin ya shafa kai tsaye.

Ya bayyana cewa, wannan al’amari mukaddari ne, amma kuma wajibi ne ga Gwamnati tabi kadin al’amarin tare da nema ma al’umma hakkin su.

Gwamnan ya kuma ja kunnen su da kada su kuskura a biyo ta bayan fage a basu kudin da basu taka karya sun karya ba da sunan an daidaita. Tare da nanata cewa duk wanda ya tunkare su da wata magana to a fito fili gaban shuwagabanni ayi ta.

Yayi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu kuma Yaba dangi da aminnai hakurin juriyar wannan rashi.

Da ya juya ta bangaren tsaro kuwa, Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa ba zai yiwu ba wasu su sayi bindigogi ba suna farautar mu gari gari mu kuma mu rungume hannuwa muna kallon su. Saboda haka mu ma mu tanaji bindigogi domin mu kare kawunan mu.

Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da sauran manyan jami’an Gwamnatin Jiha suka rufa wa Gwamnan baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

RESOLUTIONS OF THE NORTHERN STATES GOVERNORS’ FORUM MEETING WITH NORTHERN STATES EMIRS AND CHIEFS HELD ON MONDAY 27TH SEPTEMBER, 2021

The Northern States Governors’ Forum, in its continuous efforts to address the challenges bedeviling the Northern States convened an Emergency Meeting today Monday 27th...

Zaben Shuwagabannin Jam’iyyar APC a Katsina… Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan’takara:

Zaben Shuwagabannin Jam'iyyar APC a Katsina... Tsohon Ciyaman yasa mu kware Fostar Dan'takara: Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News An Ja Zare tsakanin masu neman kujerar...

ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1)

ME KAMFANIN GREEN HOUSE YAKE BOYEWA NE? (1) Sharhin jaridun Katsina City News Kamfanin da ke buga jaridun Katsina City News, jaridar Taskar Labarai da The...

BISA KUSKURE: Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20

Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20 a bisa ga kuskure Sojojin Najeriya sun sake kashe fararen hula 20 a bisaga kuskure a garin...

Zagayen Juyayin ‘Yan Shi’a: Jami’an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja

Zagayen Juyayin 'Yan Shi'a: Jami'an tsaron Najeriya sun buɗe wuta a Abuja... Rahotanni dake shigomana daga Abuja nacewa, gamayyar Jami'an tsaro, na Najeriya sun buɗe...
%d bloggers like this: