Advert
Home Sashen Hausa WAI DAMAN BABU HUKUMAR HISBA A JIHAR KATSINA?

WAI DAMAN BABU HUKUMAR HISBA A JIHAR KATSINA?

Wannan tambaya ce da mutane da yawa wadanda ba ‘yan Katsina ba suke yi musamman tsakanin shekaran jiya zuwa yau sakamakon sanya hannu ga Bill din kafa hukumar da Gwamnan Jihar Katsina yayi.

Kasancewar babu hukumar a Katsina duk da cewa a Katsina nan ne kusan tushen kafuwar Hukumar a duk inda ka ganta a Nigeria hakan ne ma ya sa mutane da yawa suke mamaki cewa ashe babu hukumar a gwamnatance.
Tabbas akwai Hisba a Katsina sai dai ba gwamnati bace ta kafa su ba, ba kuma kalkashin gwamnati take ba.

Duk da ni ban taba yin Hisba ba kasancewar na riga na shiga aikin agaji wanda hakan ya sanya mutane daga sauran jahohi idan wata matsala ta taso wadda su ka san aikin hukumar Hisba ne kai tsaye suna tuntubar mu ko su bada adireshin mu cewa azo wajan mu za mu yi abin da ya dace.
Ban mantawa akwai case na wata yarinya daga Bauchi wadda mahaifyar ta ta amso ta daga wajan mahaifinta qarshe ta mai da yarinyar gidan karuwai anan Katsina. Mahaifin yarinyar yazo Katsina da niyyar ya tafi da yarinyar karshe aka ce mai barawon yarinya dole ya hakura, yayi nufin komawa sai tunani yazo mashi ya tafi ofishin Hisba ya kai Complain qarshe sai dai aka turo shi wajan mu, lokacin da yazo yayi mana bayani muka bincika acan Bauchin muka tabbatar sai muka yi namu kokari Allah ya sa ma lamarin albarka karshe ya amshi diyarsa.
Babban abin da ya sa nayi wannan rubutu shine case na wata mata da mijin ta ya sake ta, ya bar ta da yara guda 4 wanda tun da ya rabu da ita ba ruwan shi da kula da dawainiyar yaran. Kasancewar shi a Kano yake ita kuma ta dawo nan gidan su a Katsina. Tayi zirga zirga da kai koke kala-kala amman mutumin nan yaqi ya riqa turo kudin abinci da sauran bukatu na yaran. Ba a fi sati biyu ba matar ta kirani tana kuka ta bayyana mani halin da take ciki.
Bayan ta gama yi min bayani sai tunani ya kamani cewa wadanan ayyuka da akwai hukumar Hisba da ta zamo silar share ma matar nan hawaye da ma sauran al’umma.

Akwai ma wata yarinya da ta gudu ta tafi Kano dakin saurayinta qarshe hukumar Hisba ta can Kano suka yi mana magana cikin ikon Allah mu ka samu aka maido yi ta wurin iyayen ta.
Akwai kungiyoyi masu fadakarwa kan gyaran tarbiyya, zamantakewar aure lallai suna murna da fatan kasancewar wannan hukuma.
Ita kanta Lajnatul Hisba wadda ke gudanar da ayyukan ta a jihar Katsina tsawon shekara ashirin suna murna da kasancewar hukumar.
Akwai matsaloli da yawa wanda da akwai hukumar da tuni an magance su.

Muna fatan Allah Ya sa a qaddamar da hukumar nan ba da jimawa don shi kan shi Gwamna idan yai haka ya bar wani babban alherin da Allah zai ta rubuta mashi lada akai. Bai dai wuce kwanaki dari biyar da yan kai Gwamnatin nan ta Gwamna Amin Bello ta tafi ba don haka Mai Girma Gwamna ayi gaggawar aikata wannan aikin na alheri.

Hassan Kabir Yaradua
10/11/2021
08030524842

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...