Wadanda Suka Sace Daliban Jami’a A Kaduna Sun Nemi Miliyan Dari Takwas (800)

Thesheild online

Bayanan da ke fitowa daga Jihar Kaduna na cewa Yan bindigar da suka sace dalibai 23 na jami’a mai zaman kanta a daren Jiya sun nemi a ba su kudin fansar naira miliyan dari Takwas.
Su dai Yan bindigar da suka sace daliban sun nemi a ba su kudin fansa ne ta hanyar tuntubar wasu daga cikin iyalan daliban da suka sace, inda suka ce su na son a ba su miliyan 800 kafin su sake su.
Kamar dai yadda wakilin mu ya samu damar tattara bayanai daga Kaduna cewa a Daren jiya Yan bindigar suka kutsa kai makarantar da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja mai tsawon milimita 34 daga garin Kaduna inda suka rika yin harbin kan mai uwa da wabi a cikin Makarantar.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum daya da wata majiyar ta ce mai gadi ne da aka bayyana sunansa da Mista Paul, an kuma sace dalibai 23.
Duk da ana cikin tattaunawa da iyayen yara dalibai da ke karatu a makarantar wata mai suna Georgiana Stephen ta ce Yan bindigar da suka sace yar uwarta sun nemi a ba su makudan kudi naira miliyan 8 a matsayin fansa kafin su sako yar uwarta da ke hannunsu maharan.
Za mu dai ci gaba da kawo maku rahotanni yadda lamarin ya kasance nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here