Wacece Aisha Yusufu? Matar da ta jagoranci zanga-zangar #ENDSARS acikin hijab.

Aisha yusufu matar da ta jagoranci zanga-zangar Endsars acikin Hijab

Matar da ta jagoranci zanga-zangar #EndSars a cikin hijabi

Endsars

Aisha Yesufu ta ja hankali sosai a ciki da wajen Najeriya sakamakon jagorantar zanga-zangar #EndSars da ta yi cikin hijabi.

Aisha ta jima ta na irin wadanan fafutika kan ƴan ci da kare haƙƙi. Domin ko lokacin gangamin ƙwato ƴan matan Chibok na #Bringbackourgirls ita ce a kan gaba.

Hoton da ya nuna ta cikin hijab ta daga hannu alamun a ‘ƴantar da mu’ ya kasance abin da mutane suka yi ta sara mata da namiji ƙoƙari wajen ganin an kawo sauyi kan cin zarafin da ake zargin rundunar ƴan sanda na aikatawa a ƙasar.

Mutane da dama sun yi ta wallafa hoton Aisha wacce ake ganin ta zaburar da ƴan ƙasa don sanin ƴancin su.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here