Wa Ya Kamata Ya Gaji Gwamna Masari? – Ibrahim Abdu Ghana.

Amsar wannan tambaya tana da sarƙaƙiya kuma dole sai al’ummar jihar Katsina sun yi taka-tsan-tsan wajen gano wanda ya fi cancanta da zama gwamna a zaɓukan 2023 masu zuwa. saboda su ne ke da
wuƙa da nama wajen zaɓar wanda zai gaji gwamna, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, tun daga zaɓen fitar-da-gwani har zuwa na gama-gari.

Jihar Katsina a yanzu tana da al’umma sama da miliyan goma, kuɗin da take samu daga Asusun Gwamnatin Tarayya da harajin cikin gida fiye da rabinsu na tafiya ne ga albashi da biyan fansho, adadin ma’aikata da ‘yan fanshon jihar baki ɗaya ba su haura dubu talatin da biyu ba, To a duba wannan lissafin, kenan da me sauran miliyoyin mutanen da ke jihar Katsina za su rayu? Da me za a yi wa al’umma ayyukan raya ƙasa da na more rayuwa? Abubuwan da yawa, ashe kuwa dole ne sai an yi taka-tsan-tsan kafin a san wane irin mutum ne mafi dacewa da kujerar gwamna, wanda ya san yadda zai shawo kan yanayin da tattalin arziƙin jihar yake ciki, masanin da zai buɗe hanyoyin samuwar ayyukan yi da sana’o’i, wanda zai rungumi farfaɗo da tattalin arziƙin jihar cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ba tare da al’umma ta jigata ba.

WANENE WANNAN MUTUM??

Amsar a fili take, dole a nemo masani kuma mai gogewa ta fannonin mulki da tattalin arziƙin ƙasa. Irin wannan mutum na hango haske a fuskarsa ta yadda zai kasance mafita ga al’ummar jiharmu ta Katsina. Idan na bayyana shi a matsayin tsohon malamin makaranta mai digiri a fannin ilmi, digiri na biyu (master’s degree) a fannin mulki da kuma wani digirin na biyu a fannin tattalin arziƙin al’umma, gogaggen ma’aikaci a manyan bankuna daban-daban kamar su:
_Branch Manager Standard Trust Bank.
_Branch Manager United Bank For Africa PLC.
_Mainstreet/Skye Bank Regional Manager Katsina & SokotoDa sauran ayyuka, mabambanta da suka shafi tattalin arziƙi. Shi ne ya kasance mai ba gwamna shawara a hulɗar bankuna da kuɗaɗe, uwa-uba kuma shi ne Tsohon Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙin jihar katsina ina ganin zance ya ƙare! Idan har yanzu da saura, wannan ba kowa ba ne face MALAM FARUK LAWAL JOƁE. Shi ne wanda zai farfaɗo da tattalin arziƙin jihar Katsina cikin ƙwarewa da sanin makama. An sani rashin ayyukan yi da matsin tattalin arziƙi su ne ke haddasa aikata miyagun laifukan da muke fama da su a jiharmu ta Katsina, da zarar an Ƙyautata jin daɗi da walwalar al’umma, kowa ya sami abun yi, to zaman lafiya zai dauwama, kwanciyar hankali za ta nashe ɗaukacin jiha, komai ya zama tarihi. Haƙiƙa al’ummar jihar Katsina tana muradin samun haziƙin gwamna irin MALAM FARUQ LAWAL JOBE.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here