Vorkuta birnin da mutanensa suka fice gaba daya saboda dusar kankara
Wani Birni ne a kasar Russia da ake kira Vorkuta, wanda ake zaton shine birnin da yafi ko ina tsananin sanyi a nahiyar Turai, mutannen garin baki daya sun fice sun bar gidajensu saboda tsananin sanyi da yadda kankara take zuba.
Allah daya gari bamban, lokacin da muke kukan tsananin zafi da rana, wasu na nan sanyi yayi musu yawa. Allah buway.