Covid-19: Matar da aka yanke wa hannaye da ƙafafu sakamakon kamuwa da cutar korona

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyo:

An yanke wa wata mata ƴar Birtaniya Caroline Coster hannaye da ƙafafunta sakamakon cutar korona da ta jawo mata numoniya, ita kuma ta rikiɗe zuwa cutar sepsis.

Sai da ta shafe wata guda cif a yanayi na doguwar suma a asibiti kuma sau biyu ana fitar da rai da ita inda ta kusa mutuwa bayan da ta kamu da cutar korona a watan Maris.

Ta ce a yanzu tana sa ran yin rayuwarta ta gaba cikin aminci duk da rashin hannaye da ƙafafu.

Sannan ta gargaɗi mutanen da ke raina cutar korona ko waɗanda ba sa ɗaukarta da muhimmanci kan su kula sosai.