Uwar gidan gwamnan jihar katsina ta kaddamar da rabon abin rufe Baki

Uwargidan Gwamnan jihar Katsina Hajia Dr Hadiza Aminu Bello Masari (Uwar Marayun jihar Katsina) ta kaddamar da kashi na 3 na rabon takunkumin rufe fuska (facemask) ga shuwagabannin yanki na ma’aikatar Ilimi ta jihar Katsina.

Wannna yana zuwa ne daidai lokacin da ake shirin bude makarantun firamare da na gaba da firamare a dukkan fadin jihar Katsina.

Wannan dai yana daga cikin shirin Uwargidan Gwamnan jihar Katsina Hajia Dr Hadiza Aminu Bello Masari karkashin cibiyarta ta kula da mata kananan yara ta jihar Katsina (center for the advancement of mothers and children in Katsina) hade da hadin gwiwar kamfanin green house Katsina domin samar da wannan abin rufe fuska (Facemask) huda miliyan daya (one million facemask) domin taimakawa wurin yakar wannan cuta ta coronavirus (covid-19).

An raba wadannan abin rufe fuska (facemask) ne da shuwagabannin shiyya (zonal directors) na ma’aikatar Ilimi ta jihar Katsina.

Shugaban kwamitin amintattu na wannan cibiya babban jojin jihar Katsina mai shari’a Musa Dalladi Abubakar ya bayyana irin kokarin da wannan cibiya ta yi tun farko na yadda wannan baiwar Allah ta kirkiro shirin samar da takunkumin rufe fuska (facemask) guda miliyan da doriya kyauta domin raba ma bayin Allah, hakan duk ya farune domin sakamakon irin kokarin da take na ganin ta tallafa ma Ilimi a kowane irin mataki.

Shugaban kwamitin kartakwana na jihar Katsina akan wannan cuta ta coronavirus kuma babban sakatare na ma’aikatar lafiya ta jihar Katsina Dr Kabir Mustapha ya yaba ma tunanin wannan baiwar Allah na ganin tayi abinda babu wanda yayi shi na kawo dauki domin ganin an dakile yaduwar wannan annoba ta coronavirus.

Kwamishiniyar kula da harkokin mata ta jihar Katsina Hajia Rabi’atu Mashi a na ta jawabin ta roki al’umma da suyi amfani da wannan facemask din ta hanyar da ta dace, kuma su bi dukkan ka’idojin da hukumomin lafiya suka ba da domin ganin an kawar da wannan annoba.

Kwamishinan ma’aikatar Ilimi na jihar Katsina Farfesa Badamasi Lawal Charanci, a na sa jawabin, ya ba da tabbacin za suyi amfani da wannan gudummuwa, za su ba uwaye da malamai shawara akan yadda za su kara kare kan su daga wannan annoba.

Uwargidan Gwamnan jihar Katsina Hajia Dr Hadiza Aminu Bello Masari (Uwar Marayun jihar Katsina) tayi godiya ga daukacin mutanen da suka tsaya dare da rana domin ganin an tabbatar da samar da takunkumin rufe fuska (facemask) miliyan daya da doriya, musamman yan kwamitin amintattu na cibiyar kula da mata da kananan yara ta jihar Katsina da sauran mutanen da suka taimaka wurin ganin wannan al’amari ya tabbata.

Kashi na hudu yana zuwa nan gaba lokacin da za’a raba na kananan yara yan firamare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here