@Katsina City News
Majiyoyi masu karfin gaske dake da alaka jami’an tsaro masu sanya Ido da tattara bayanai akan masu aikata, miyagun laifuffuka sun tabbatar ma da Jaridun Katsina City News, cewa anga wasu Babura kamar guda arba in sun baro Dutsen Sola garin shahararren Dan ta addar nan mai suna Adamu Aleru, sun tunkaro jahar Katsina.
Wasu kauyukan da masu Baburan suka bi, wani Ɗan sa kai ya tabbatar ma da Jaridun mu cewa sun Kirga Babura 40 kowane Babur da goyon daya-daya.
Wata majiya tace, sun rika haduwa da wasu Baburan akan hanya suna hadewa dasu.
Majiyarmu tace, yaran Aleru sun fita daga dajin Zamfara ya zuwa lokacin wannan rahoton suna cikin dajin jahar Katsina.
Majiyarmu tace, Babu Wanda yasan ina zasu kai Kari? Ko kuma ina suka dosa?
Adamu Aleru, shine Wanda aka ba sarkin Fulanin daji a jahar Zamfara, kuma yana da kyakykawar alaka ta sulhu da Gwamnatin jahar Zamfara.
Wadannan miyagun ko ina suka dosa? Ko ina zasu kai Hari? Allah yayi maganin su.
Katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245