Yan sanda na riƙe da waɗanda ake zargi da wawure kuɗi a gidan gwamnatin Katsina
Jami’an tsaro a Jihar Katsina na tsare da wasu ma’aikatan gwamnatin jihar da ake zargi da sace maƙudan kuɗi a gidan gwamnati.
Shugaban sashen hulɗa da jama’a na Gwamnatin Katsina, Al-Amin Isah, ya tabbatar da cewa kusan mako biyu ke nan da faruwar lamarin, ba kamar yadda wasu kafofin yaɗa labarai suke ruwaito ba.
Da yake tabbatar wa BBC Hausa faruwar lamarin, Al-Amin bai bayyana adadin kuɗin ba, yana mai cewa waɗanda abin ya shafa za su yi ƙarin bayani.
Zuwa yanzu an saki wasu daga cikin ma’aikatan sashen kuɗi da masu gadi da aka kama yayin da ake ci gaba da riƙe wasu, waɗanda hukumomi ba su bayyana adadinsu ba.