Kotun kula da ma’aikatu NIC ta bukaci kungiyar Malaman jami’o,i da Gwamnati su gurfana a gabanta
A yau Litinin ne kotun kula da Ma’aikatun Najeriya ta bukaci kungiyar malaman Jami’a da Gwamnati su gurfana a gabanta a Abuja domin jin bayanai game da yajin Aikin malaman jami’o’i da yaki ci yaki cinyewa, wanda ya tsaida harkokin karatun jami’o’in tun a cikin watan Fabrairu. Aikawa wadannan bangarorin da kotun tayi ya biyo bayan mika koken na Kungiyar ASUU da Gwamnatin tarayya tayi ga kotun ma’aikatun wanda Ministan Kwadago Chris Ngige yayi.
Gwamnatin tarayya tana fatan Kotun ta baiwa kungiyar ta ASUU umarnin komawa bakin Aiki.
Daga cikin wadanda aka aikawa Sammacin don su bayyana a gaban Kotun akwai Ministan Ilimi, da na Shari’a da Ministan Kwadago da kuma shugaban kungiyar ASUU na kasa.