A karon farko wata mata ta haifi ‘ya’ya 5 ringis cikin koshin lafiya a karamar hukumar Faskari jihar Katsina
Daga Ibrahim M Bawa
Wata mata mai suna Hajara da mijinta mai suna Sha’aibu a cikin garin Doma A, gundumar mazabar Tafoki cikin karamar hukumar Faskarin jihar Katsina ta haifi ‘ya’ya biyar ringis a daren jiya Talata.
Kansilan mazabar Tafoki Hon Abdullahi Currency ya tabbatar wa Katsina Media Post da faruwar lamarin, inda ya ce “Yanzun haka maganar da nake da kai, muna tare da matar a babbar asibitin Funtua, kuma jariran da uwar suna karkashin kulawar asibitin”
“Matar kuma sami maza uku, da mata biyu” Inji kansilan
Sai dai matar na bukatar taimakon gwamnati da al’umma, na yadda za a tallafa mata don ganin yaran sun rayu cikin koshin lafiya, duba da yadda ita kadai ba za ta iya shayar da jariran ba, sai da tallafin kulawar likitoci
A iya cewa wannan ne karon farko da aka sami matar da ta haifi ‘ya’ya biyar a jihar Katsina, duk da an taɓa samun wadda ya haifi yan hudu a wurare da dama a cikin jihar.
