A cewar kafar yada labaran Spain El Nacional, Lionel Messi bai ji dadin yadda shugaban PSG Nasser Al-Khelaifi ya ki sayan dan wasan Barcelona Jordi Alba a bazara ba.
Da alama kungiyar ta Catalan suna neman cire shi daga litattafinsu, tare da babban kocin kungiyar Xavi baya amfani da shi sosai a kakar wasa ta bana, inda ya fifita Alejandro Balde mai shekaru 19 tare da kawo Marcos Alonso.
Alba ya buga wasanni uku a gasar La Liga kawo yanzu, wanda ya fara sau daya kacal kuma ya ga jimlar mintuna 126 na taka leda yayin da makomarsa a kungiyar ke kan tashi.
Lionel Messi yana sane da yunkurin da Barcelona ke yi na siyar da dan wasan kuma ya so Parisians su nemi dan wasan na Spaniya.
Duk da haka, El Nacional ta kara da cewa Al-Khelaifi yana jin matakan Alba a cikin ‘yan shekarun da suka gabata ba su da ban sha’awa yayin da dan wasan na baya na hagu ke gab da yin ritaya.
Messi, ko da yake ya ji takaicin yadda kulob dinsa ya ki amincewa da bukatar tsohon abokin wasansa, amma ya amince da shawarar da suka yanke.
Ko da ya iya komawa PSG, Babu tabbas Alba na shiga kungiyar farko kamar yadda babban koci Christophe Galtier ya amince da Nuno Mendes.
Hakanan yana da Juan Bernat a matsayin zaɓi a wannan matsayi, yayin da Achraf Hakimi da Presnel Kimpembe suma suna iya aiki daga matsayi na hagu.
Alba yana da sauran shekaru biyu a kwantiraginsa da Barcelona, ​​amma da alama lokacinsa na shiga kungiyar farko ya kare, sabon dan wasan da kungiyar ta dauko Marcos Alonso shi ma yana gabansa a cikin jerin gwanon samun gurbi.