Muazu Hassan @Katsina city news
Yanzu ta tabbata jam iyyar PDP tana da shugabanni biyu a jahar .
Na farkon su, shine Alhaji Salisu lawal Uli Wanda ke rike da shugabancin mataimakin shugaban jam iyya na jaha.
Shine Wanda tsohon shugaban jam iyyar Alhaji salisu Yusufu majigiri ya rubuta ya mika masa ragamar shugabancin tsawon lokaci.
Majigiri, ya fada ma jaridun katsina city news cewa ya Dade da rubuta takardar ajiye aiki da mika ragamar tafiyar da jam iyyar ga mataimakin shi Alhaji salisu Uli.
Majigiri, yace duk hayaniyar nan, uwar jam iyya ta San, bani bane shugaban jam iyya a katsina. Domin tuntuni na bada mataimaki na.shiru nayi inga gudun kowa.
Shugaba na biyu shine .Alhaji lawal magaji Danbaci .matsayin shi ada shine, mataimakin shugaban jam iyya na shiyyar funtua. Wanda a taron da akayi a gidan Yakubu lado Dan marke a Kano aka nada shi.
Yanzu kallo ya koma sama, ba asan da wa uwar jam iyya ta kasa zatayi aiki ba .shin Uli ne ko Alhaji lawal magaji?
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email:[email protected]

