Shugaban hukumar Zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ya bayyana cewa Babban abinda hukumar ta sanya a gaba yanzu shine samar da kayan aiki da adanasu, sana kuma da rabasu inda ya dace idan lokaci yayi. Farfesa Muhamud Yakubu yayi wannan jawabin ne a lokacin da yake rantsar da yan kwamitin kula da muhimman kayayyakin zabe a Abuja. Yakubu ya kara da cewa Shirye-shirye sunyi nisa domin tunkarar zaben watan Afrilu na shekarar 2023. Yace hukumar bata da niyyar daga Zaɓen ƙasar, yace hukumar zatayi hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin gudanar da Sahihin zabe.
Source:
Katsina City News
Via:
Katsina City News