Physiology Hausa
Karayar ƙoƙon gwiwa na faruwa sakamakon bugu daga faɗuwa, faɗowa ko haɗuran ababen-hawa. Karayar ƙashin ƙoƙon gwiwa na iya zama rabewa gida biyu ko uku ko kuma fiye da haka.
Bayan tabbatar da karayar ƙoƙon gwiwar ta hanyar dubawa da gwaje-gwaje, ana yin tiyata domin ɗora ƙashin ƙoƙon gwiwa. Galiban ana yin ɗorin ne ta hanyar ɗaure karyayyun ƙasusuwan da wata waya ta musamman zuwa lokacin da karayar za ta warke daga bisani kuma a cire wayar.
Duk da cewa ba kasafai ake samun karayar ƙoƙon gwiwar ba, domin baya wuce kaso ɗaya cikin ɗari na karayar ƙasusuwa.
Sai dai, karayar ƙoƙon gwiwa na zuwa da ƙalubale na riƙewar gwiwa bayan tiyatar. Ƙarin matsalolin da ke biyo bayan tiyatar sun haɗa da ciwo, kumburi, rauni ko rashin ƙwarin ƙafar da kuma wahalar tafiya musamman saboda gwiwar ba ta lanƙwasuwa sosai.
Bayan kowace tiyatar ƙashi, muradin shi ne majinyaci ya dawo aiki da gaɓar yadda ya kamata. Sai dai wannan muradi na iya gamuwa da cikas idan ba a samu kulawar likitan fisiyo ba. Ana so majinyaci ya fara samun kulawar likitan fisiyo da zarar an yi tiyatar.
Wannan zai taimaka wajen rage ciwo, kumburi, rauni, shanyewa ko sirancewar tsokokin cinya da kuma uwa-uba riƙewar gwiwa.
Aikin likitan fisiyo na dawo da aikin gaɓa bayan tiyata shi ne tagomashin tiyatar kanta!
Saboda haka, akwai buƙatar samun kulawar likitan fisiyo ga majinyacin karayar ƙoƙon gwiwa ko kuma ma duk wata karaya da ke iya janyo riƙewar gaɓa.