
Dubun dubatar Magoya bayan jam’iyyar APC daga kananan hukumomin Safana, Kurfi, Dutsin-ma, Danmusa da Batsari ne suka yi Rudda daga jam’iyyar su ta APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP, inda aka shirya gagarumin taron karbar su a garin Safana cikin jihar Katsina a karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar ta PDP Hon. Salisu Yusuf Majigiri.
Taron da ya gudana a ranar Lahadi 11 ga watan Satumba 2022 ya hada dukkanin jagororin jam’iyyar PDP da Sakataren jam’iyyar na Ƙasa Sanata Ibrahim tsauri, Dantakarar Gwamnan jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke, Dantakarar Sanatan Katsina ta tsakiya, Engr. Surajo Aminu Makera, Shugabannin jam’iyyar PDP na yankuna da na kananan hukumomi, Hon. Musa Gafai Shugaban kungiyar Ladon Alkhairi da sauran ‘Yan kungiyoyi daban-daban.
An gabatar da wakilan ‘yan jam’iyyar na APC da suka fice daga cikinta zuwa PDP sun gabatar da wajabai akan dalilansu na ficewa daga jam’iyyar APC, kuma sun tabbatarwa shugabannin jam’iyyar na PDP cewa su makamai ne, mayakan na baya, kuma zasu shigo Kwanannan zasu yaki jam’iyya mai mulki.
Tun da farko mai masaukin baki Shugaban jam’iyyar PDP na Ƙaramar hukumar Safana, Hon. Illela ya gabar da jawabin maraba da baki, daga bisani kuma shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina ya yi jawabin godiya ga al’ummar da suka taru wajen gami da kira a garesu da suyi PDP daga sama har kasa.
Da yake jawabi a madadin dukkanin’yan takarar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke yace; “Yanzu Al’umma sun gane inda aka dosa, yace babu ma kamar Æ™aramar hukumar Safana, tana daya daga cikin garuruwan da suka dandana azabar mulkin APC yace ba sai an fadi masu illar ta ba. A karshe yayi fatan Allah ya kawo lokacin da za’a dunga Sayen Shinkafa buhu dubu bakwai manja dubu biyar.