
A wani yunkuri na samar da yanayin da zai bada dama Mutane su iya lura da shige da ficen bakuwar Fuska a cikin Unguwannin Birnin Katsina, musamman da daddare, domin inganta tsaro, Dantakarar kujerar Majalisar wakilai ta tarayya karkashin jam’iyyar PDP a karamar hukumar Katsina, Hon. Aminu Chindo (Sadaukin Katsina) ya samarwa kowace mazaba a karamar hukumar ta Katsina Lantarki mai aiki da hasken rana. A inda za’a cigaba da kafasu a cikin birnin Katsina, Hon. Cindo ya bayyana aniyar sa ta cigaba da wadata garin Katsina da wannan Lantarki na Sola, inda yace da yardar Allah ko ina a cikin Mazabar Katsina tallafin hasken zai shiga, amma yanzu za’a fara badawa a yankunan mazabu na cikin Birni. Hon. Chindo da ya samu wakilcin Alhaji Shehu Kofar Sauri, kuma Shugaban Elders na karamar hukumar Katsina, ya bayyana Aikin sanya Fitilun zai kasance a karkashin jagorancin Uwar jam’iyyar PDP da Ciyaman da Kansilolinshi. An gudanar da taron bisa jagorancin shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Katsina da dukkanin Kansiloli goma sha biyu dake karamar hukumar da shugabannin jam’iyyar PDP na mazabu (Ward) a gidan ÆŠantakarar Hon. Aminu Chindo dake Bayan gidan Dikko Inde a cikin birnin Katsina, wanda ake saran ÆŠantakarar Gwamna Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke zaizo ya fara aza harsashen sanya Fitilun.