A zaman majalisar na ranar labara 24 ga watan Agusta, Gwamnatin ta amince da kashe kudin don Samar da Kayayyakin cigaban Al’umma a kananan hukumomi goma Da aiyukan ‘yan Bindiga ya shafa.
Mai bawa Gwamnan jihar Katsina shawara akan Dabbobi da gandun Daji Dakta Lawal Usman bagiwa ya sanar da hakan ga manema labarai Bayan kammala zaman Majalisar da aka saba gudanar wa duk sati Wanda Gwamna Aminu Masari yake jagoranta.
Kamar yanda ya bayyana, ayyukan da za’a aiwatar sun hada Gina makarantu Fulani da Masallatai Hanyoyi da sauransu, a garuruwan Jibiya, Batsari, Safana, da Danmusa. Sauran sun hada da Kurfi Dutsin-ma, Faskari, Sabuwa, Kankara da Dandume. Wanda dukkanin su zasu amfana da Ayyukan.