Layin wutar lantarki na ƙasa ya sauka gaba ɗaya, inda ya zama babu megawatts (MW) ko ɗaya, tun da karfe 10:51 na safiyar yau Litinin, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki a fadin kasar baki daya, inji rahoton Daily Trust.
Wannan ci gaban ya faru ne kwanaki kaɗan bayan masu amfani da wutar lantarkin wutar ta samu sosai a ƙasar.
Tashar wutar lantarki ta kasa da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin ta samu megawatt 3,712 da aka samar daga kamfanoni 21 na rarraba wutar lantarki (GenCos) kafin ta koma 0MW bayan awa daya.
Bisa ga bayanin da aka samu daga tumbin yaɗa bayanai na wutar lantarki, wani sashe na Kamfanin Rarraba Wutar lantarki (TCN), Afam IV ne kawai a kan layin wutar, amma ba tare da an samu komai na wutar ba har zuwa karfe 12 na rana.