Jaridar Amana August 26, 2022

A yayin da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya shawo kan takaddama da ya shiga a Jihar Borno, bayan rufe ofishin jam’iyyarsa da kuma kama dan takarar Sanatanta, sai ga shi tabka wata babbar asara a Jihar Yobe, inda dan takarar mataimakin Gwamna a NNPP ya koma APC.
Hon. Yahaya Gamajeji ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC ne a yau Alhamis, yayin da ya je wajen Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni ya bayyana ya bar tafiyar Kwankwasiyya.
Kazalika, Gwamna Mai Mala Buni ya amshi wani babban jigo a jam’iyyar PDP a jihar ta Yobe, Alhaji Sa’idu Sadauki Gashuwa, wanda shi ma ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda jaridar Alkuki Hausa ta ba da rahoto.

Majiyar tamu ta bayyana cewa, Gwamna Buni ya karbe su ne tare da Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka, kamar yadda babban Daraktan Yada Labarai na Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mamman Mohammed ya bayyana