
Muazu Hassan @Katsina City News
Wasu masana da kwararru da kamfanin jaridun Katsina City News ya nemi su yi nazarin kundin da dan takarar jam’iyyar APC, Alhaji Dikko Umar Radda ya gabatar a matsayin tsarin da zai bi wajen mulki Katsina in har ya ci zabe, sun yi kira da dan takarar ya sake karatun kundin, kuma ya tuntubi masana a kansa, sannan ya yi fatali da shi.
Masanan karkashin wani tsohon shugaban ma’aikata na Jihar Katsina da tsaffin manyan sakatarorin Jihar da wasu malaman Jami’a, sun ce kundin wani labari ne mai kama da Shafa Labari Shuni.
Suka ce kamar mai keke ne, wanda bai san mota ba, bai tambayi ilmanta ba, bai taba mallakarta ba, ba shi da ita, amma ya rubuta littafin koyon tukin mota.
Masanan sun ce, kamata ya yi kwamitin yakin neman zaben APC su nemo kundin rahoton da Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Ballo Masari ya tattara a kakar zaben 2015.
Suka ce, wannan kundin ya fadi komai a kan matsalar Katsina, in ban da tsaro, wanda a lokacin bai dau sabon salo kamar yanzu ba.
Masanan sun kara da cewa, ya kamata kwamitin yakin neman zaben Dikko Radda ya bi wadannan tarin rahotonni da aka tara tun lokacin, a dau na dauka.
Sun yi nuni da cewa, akwai kuma wasu jerin littattafai da Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya rubuta a kan Katsina da matsalolinta. Littattafan an gabatar da su a watan Mayu na wannan shekarar.
Littattafai ne guda biyar. Suka ce su ma akwai abin dauka a cikinsu. Don an gina su ne bisa binciken daga kasa zuwa sama.
Masanan suka ce, a shekarar 2006 gwamnatin Katsina ta kaddamar da wani bincike a kan ci gaban Katsina, su ma in suka yi nazarinsu za su taimaka masu matuka.
Rahoton yana da muhimmanci kwamitin yakin neman zabe na APC ya yi nazarinsa, in ji masanan.
Kwararrun sun yi kira da dan takarar APC ya yi fatali da wannan kundin, wanda zai iya jawo wa Katsina dariya in har aka shiga cikinsa aka yi nazarinsa sosai.
Suka ce domin an san Katsina gidan ilmi ne da bincike. Gidan masana ne da manazarta.
Hatta a harshen Turanci da aka yi amfani da shi wajen rubuta kundin, masanan sun gano kurakuran harshe 1600.
Masanan sun ce, ba sun kawo gyara ba ne don tallata wata jam’iyya ko wani dan takara, sai don maganar Katsina da ci gabanta. Suka ce, kuma gyara kayan ka, bai taba zama sauke mu raba ba.
Katsina City News za mu buga cikakken rahoton masanan nan gaba kadan.
Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email. [email protected]