Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a yau Talata ta baiwa Hukumar Ƴan Sandan Farin Kaya, DSS damar su cigaba da riƙe Tukur Mamu, mai sasanta wa tsakanin ƴan ta’adda da iyalan wadandaa akai garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja-Kaduna, har tsawon kwanaki 60.
Mai Shari’a Nkeonye Maha ya bada umarnin ne biyo bayan lauyan hukumar tsaro ta farinkaya ya nemi da a kara musu lokaci don cigaba da binkice akan Tukur.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa ‘yan sandan Masar sun kama Tukur Mamu tare da iyalansa a ranar 6 ga watan Satumba, ya yin da yake kan hanyar sa ta zuwa Saudiyya domin yin Umara, daga karshe suka dawo dasu gida Najeriya.
A ranar Lahadin ta gaba ta jami’an na hukumar ta DSS suka jawa ‘yan Najeiya kunne kan tufar albarkacin bakin su akan kama Tukur Mamu.