Kwamitin Koli na Jam’iyyar PDP na ƙasa (NWC) ya dakatar da tsohon Gwamnan jihar Barr. Ibrahim Shehu Shema da wasu mutane guda 5 daga jam’iyyar PDP bisa zargin yi ma jam’iyyar zagon ƙasa a jihar Katsina.
“Katsina Reporters ta samu rahoton cewa bayan zuzzurfan bincike da ƙwamitin ya gudanar akan sha’anin abinda ya shafi dokokin Jam’iyyar bisa sahalewar kundin tsarin mulki na (2017) an miƙa Gwamanan Jihar Benue Dr. Samuel Ortom da Shema da tsohon Gwamna Fayose da Anyim zuwa ga kwamatin da’a na dakatarwa na ƙasa biyo bayan korafe-korafe na yi ma jam’iyyar zagon ƙasa.
Haka zalika, ƙwamitin (NWC) har ila yau ya dakatar da wasu mutane 5 daga jam’iyyar daga ranar Alhamis 23 Maris, 2023.
Sa Hannu :
Hon. Debo Olugunaba
Jami’in watsa Labarai na ƙasa.