
Ta bakin jami’in hurda da jama na jam’iyyar a taronsu na ranar Alhamis a Ofishin da suka kira halastaccen Ofishin Jam’iyyar na NNPP wanda Dantakarar Shugaban ƙasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bude da hannunsa. Hon. Nasiru Usman Kankia ya bayyana cewa “Mune Kadai halastaccen ‘Ya’yan jam’iyya NNPP wadanda ba muyi butulci ba bamuci Amanar Jam’iyya ba da mu da dukkanin ‘Yantakarar kujeri na kananan hukumomi, da shugaban mu Injiniya Nura Khalil.” Yace wasu maciya amana ne suka saida jam’iyyar ana saura kwanaki kadan zaben Gwamna, kuma dama Dantakararsu na shugaban ƙasa bai gamsu da shugabancinsu ba, shiyasa yaki yarda ya tura masu kudin mutane don gudanar da aikin jam’iyya.
Hon. Kankia yace, “mun shigar da Kara domin Kotu ta tabbatar mana da cewa mune muka zo na uku a zaɓen Gwamna, kuma abinda ya bayyana cewa Jam’iyya APC da Dantakarar su bai aje Mukaminsa ba kamar yanda Doka ta tanada idan mutum zaiyi takara, don haka Kotu zata bayyana shi a matsayin wanda ba halastaccen dan takara ba,” yace ita kuma jam’iyyar PDP rikicin shugabanci ya dabaibayesu sun kasa fidda shugaba balle har a sanyasu cikin jerun jam’iyyar da ke takara, don haka wannan shine dalilin da muke ganin shari’a zatai watsi da takarar su.” Inji Kankia.
Don haka muna saran mune zasu amshi kujerar Gwamnan jihar Katsina da yardar Allah, don Dantakarar mu, na Gwamnan Injiniya Nura Khalil ba gara ba zago halastacce ne, shi yasa na sukai ta kulli dob yace ya fasa takarar saboda abinda suka hango. Inji Kankia.
Zaman da suka gudanar a Ofishin yakin neman Zaben Injiniya Nura Khalil dake Daura a Ofishin Nepa a Katsina ya hada wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar na yankuna, kananan hukumomi da mazabu da wasu daga cikin ‘Yan takarar Majalisar jihohi, a karshe sun bayyana yanda zasu iya bada gudunmawa akan wasu kananan hukumomi da ake za a sake zabe, irinsu Kankara da Kankia.