Gwamnatin Katsina Ta Hana Malamai Cinzarafin ‘Yan Firamare Da Sakandire
Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da wani yunƙuri na kawo ƙarshen ladabtarwa da ake yi wa ɗalibai a makarantun Katsina, wanda sun ce matakin da ake ɗauka na ladabtar da ɗaliban kan janyo ɗaliban su daina zuwa makarata saboda tsoratarwa, kamar yadda Katsina Post ta rawaito.
Shugaban Hukumar Ilimi na bai ɗaya ta jihar Katsina, Alhaji Lawal Buhari Daura, ya yi gargadin cewa; “daga yanzu duk shugaban makaranta ko malaman da aka samu suna azabtar da ɗalibai, to su sani za a hukunta su,”
Ya yi wannan jawabi ne a wajen taron wayar da kan jama’a game da kawo ƙarshen ladabtarwa a makarantu, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da suka haɗa da zaɓaɓɓun ɗalibai daga sassa daban-daban na yankin, wanda aka gudanar a ranar Alhamis a jihar Katsina.
Shugaban Hukumar Ilimin ya ce, hukuncin da ake yi ga jikin ɗan adam yana
haifar da babban ƙalubale na tsawon shekaru da dama, domin matakin gyara ɗaliban da suke yi kuskure ta wannan hanyar yana taimaka wa ne kawai wajen ƙaruwar yawan yaran da ke barin zuwa makaranta don nuna bajirewa ga ilimin, kamar yadda Katsina Post ta samu labari.
Ya bayyana hukuncin kallon rana, da kuma saka ɗalibi aiki tuƙuru, duk waɗannan cin zarafi ne da kuma amfani da kalaman ɓatanci ga ɗalibai.
“Waɗannan binciken na da matukar tasiri ga tsarin ilimi a Najeriya da kuma cimma burin da ake so a cimmawa mai ɗorewa”.
Hukuncin jiki kamar yadda aka saba amfani da shi a makarantar shi ne, amfani da ƙarfi ga ɗaiɗaikun ɗalibai ko nuna fifiko ga na ƙasa da kai, ko ka saka shi aiki ɓa ladabtarwa don kana sama da shi, to ba shi ne gyara ɗa’a ga ɗalibin da yaga yafi ɗan uwansa ɗalibi girman aji ba”.
“Masu aikata laifin yawanci shugabannin makaranta ne, malamai, ko kuma shugabannin ɗalibai, waɗanda ke masu cin zarafin da abin ya shafa da kuma wanda bai shafa ba”, inji shi.