Gwamnatin jihar Katsina zata inganta makarantun tsanya domin zama daidai da Zamani, shugaban hukumar Ilimin Bai daya na jihar Katsina Alhaji Lawal Buhari Daura ya bayyana haka a yayin da yake jawabi a wani taron wuni guda na masu makarantun Allo da Islamiyyu a dakin taro na Multipopse ke filin Samji cikin birnin Katsina Alhaji Lawal Buhari da ya samu wakilcin memba na biyu a hukumar Ilimin bai daya, Alhaji Ashiru Sani Batsari ya bayyana cewa taron wani kira ne daga hukumar Ilimin Bai daya uadin gwiwa da hukumar ta jiha da zai wayar da kan masu rike da makarantu akan muhimmancin inganta makarantun Allo da na Islamiyya da kuma samar da dubarun koyon sana ‘o,i ga Dalibai. Shugaban tawagar Aiwatar da shirin Alhaji Yusuf Habibu ya bayyana cewa; shirin ya fara tun a shekara ta dubu biyu da sha takwas a jihohi tara na tarayya inda makarantu sha biyar suka amfana da tallafin gine-gine na Azuzuwa Miliyan dari da sha biyar da kujeri da teburan karatun dalibai, da wajen bayan gida da dakunan karatun Al’qur’ani mai girma.
A jawaban su daban-daban Farfesa Abdulrahaman ado daga sashin koyar da Larabci da Addinin Musulunci na jami’ar Ummaru musa da Dakta Muhamud Adeza daga jami’ar Danfodiyo Sokoto sunyi jawabi akan muhimmancin inganta Ilimin tsarin tsangaya.
A jawabin godiya jami’an shirin Alhaji Musbahu Na’iya yabawa hukumar Ilimin Bai daya da masu makarantun Allo akan samun nasarar da ake bukata.