Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga masu rike da mukaman gwamnati dasu dage kan gabatar da shirye shirye da kudurorin da za su kara kyautata rayuwar al’umma karkashin tsarin gwamnatin APC na mayar da al’amurra kan muhallan da suka dace (Restoration Program).
Gwamnan yayi wannan kiran ne a jawabin da ya gabatar bayan rantsar da Alhaji Bature Umar Masari a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan gidan gwamnati da kuma Alhaji Bishir Gambo Saulawa a matsayin Kwamishina.
Alhaji Aminu Masari ya kuma hori masu rike amanar al’umma dasu rika sauke nauyin dake kawunan su da sanin cewa za su maida bayani gobe kiyama gaban Allah Ta’ala.

