
Sufeto-Janar na ƴan sanda, IGP Usman Alƙali Baba a ranar Alhamis ɗin 15/12/2022 ne ya gana da shugabannin ƴam Sanda.
Shugabannin rundunonin ƴan sanda da tsare-tsare sun taru ne a hedikwatar rundunar dake birnin tarayya Abuja, domin tantance ayyukan ƴan sanda a cikin shekara mai fita.
Bugu da ƙari tare da saita manufofin ‘yan sanda na shekarar 2023 da kuma duba tsare-tsaren harkokin tsaro na zabe, gabanin babban zaben 2023.