
Tiyata tamkar yaƙi ce — sai ta zama dole ake yin ta! Haka nan, ko da an yi nasara a yaƙin, ana iya rasa sojoji. Har wa yau, Bahaushe na cewa, “ba a ɓari, a kwashe dai-dai’.
Daga cikin matsalolin da ke biyo bayan karayar ƙashi akwai lahanin jijiyoyin laka. Lahanin jijiyoyin laka na afkuwa ta sabuba uku kamar haka:
- Lahani yayin ko bayan karayar ƙashi. Hakan na faruwa idan ƙashi ya karye sannan kaifi ko tsinin karyayyen ƙashin ya yanki ko ya soki jijiyar laka da ke kusa.
- Lahani daga akasin tiyatar ƙashi. Ana iya samun akasi ko cikas yayin fiɗa a taɓa jijiyar laka.
- Rashin kyakkyawar kulawa bayan tiyatar ƙashi. Tiyatar ɗorin ƙashi na buƙatar sanya filasta ko ƙarfe, a wasu lokutan kuma a saƙale hannu ko ƙafar. A kowane irin hali, ana buƙatar taƙaita motsin wannan sashi ne domin ba wa karayar damar warkewa.
Sai dai, bayan buƙatar taƙaita motsin sashin da ya karye domin warkewar karaya, taƙaita motsin shashin jiki ko gaɓa na da komabaya. Domin yana iya janyo shanyewar tsokoki da jijiyoyin laka, ƙagewar gaɓoɓi, tantanan gaɓa da jijiyoyin tantanai.
A duka yanayai ukun, shanyewa ko raunin jijiyoyin laka da tsokoki ne ke faruwa. Yayin da karaya ke ci gaba da warkewa bayan tiyatar ƙashi, likitan fisiyo na cigaba da kula da majinyaci domin kiyaye shanyewar tsokoki da jijiyoyin laka, kiyaye ƙagewar gaɓoɓi tare da farfaɗo da aikin jijiyoyin laka da tsokokin da suka gamu da akasin fiɗa domin a ci ribar tiyatar ɗorin ƙashin daga ƙarshe.
Bayan tiyatar ɗorin karaya, tabbatar kana samun kulawar likitan fisiyo tun da farko domin kauce wa afkuwar waɗancan matsalolin da aka ambata a sama.
©Physiotherapy Hausa