Wani Kwararre akan samar da abinci mai gina jiki na ofishin asusun tallafawa kananan yara na Majalisar ɗinkin Duniya mista dabya ziyarci Kano mista Odine Oyodefun ne ya bayyana haka a yayin taron wayar da kai na kungiyar ‘Yanjarida akan shayar da jarirai Nonon Uwa zalla da gidan Talabijin na Abubakar Rimi da ke Kano ya shirya hadin gwiwa da tallafin Asusun na UNICEF.
A cewar masanin “Kafafen yaɗa labarai nada rawar da zasu taka wajen kira ga Gwamnati da masu ruwa da tsaki da su samar da kudade da za’a gudanar tare da tabbatar da cewa ambi Dokokin shayar da Nononnuwa zalla daga watanni shida na haihuwa masanin a harkar Abinci yace a shekarar ta 2018 wani bincike da masana suka gudanar ya bayyana cewa akwai sama da yara miliyan uku yan kasa da shekaru biyar a kano.
Domin cimma nasarar da akasa a gaba Darakta General ta gidan Talabijin din Abubakar Rimi dake Kano hajiya sa’a Ibrahim tace; akwai bukatar kafafen yaɗa labarai su riƙe yin bincike akan muhimmancin shayar da Nonon Uwa zalla da fadakar da iyaye da masu ruwa da tsaki akan illar rashin shayar da Nonon uwa zalla. Tace shayar da Nonon uwa zalla na Watanni shida zai rage matsalolin yawan mace-mace ga ƙananan yara gami da cutar Tamowa.
A nashi jawabin tun da fari mataimakin Darakta na hukumar samar da lafiya a matakin farko na jihar Kano Malam murtala Inuwa yace, ana fara shayar da yaro ne dazarar an haife shi, duba da cewa da zarar an haifi yaro babu wani abinci da zai bashi dukkanin wata kariya kamar Nonon Uwa.
A jawabinsa jami’in hulɗa da jami’in hulɗa da jama’a na ofishin UNICEF dake Kano Mr Samuel Kalu yace an shirya taron ne domin bikin Makon shayar da yara Nonon Uwa. Yace taron zai taimaka wajen baiwa ‘Yanjarida dama domin su kara tabbatar da ana shayar da yara Nonon Uwa zalla.