An kaddamar da fara shirin bayar da horo ga jami’an sintiri har su dari shida da suka fito daga ƙananan hukumomi 34 dake fadin jihar Katsina.
An kaddamar da fara basu horon ne a sansanin horar da jami’an Sibil difense dake nan cikin birnin Katsina a yau Laraba.
Mai taimaka wa Gwamnan jihar Katsina a kan sha’anin tsaro Alh Ibrahim Katsina, ya ce an dakko mutum dari shidan ne a duk fadin jihar Katsina kuma maza da mata da suka aminta da samun horon da kashin kansu.
Ya ce tun da farko an fara ba yan bijilantai 500 irin wannan horon, yanzun kuma 600 sun shiga, nan gaba kuma za a kara jami’ai 1900 da za su sami irin wannan horon.
Ibrahim Katsina ya ce za a basu horon tunkarar yan bindiga ba sai sun shigo cikin garuruwa ba, kuma za a basu horon koyon sarrafa makaman zamani.