A rahoton da Katsina City News ta samu ya nuna cewa a Ƙaramar Hukumar Safana a Mazaɓar Ɓaure Ba a samu gudanar da zaɓe ba kamar sauran yankunan.
Ɓaure B mai Rumfunan zaɓe kusan goma, sun fuskanci Cikas daga Ɓarayi masu Garkuwa da Mutane, inda sukace ba zasu bari a yi zaben ba sai ambasu dubu ɗari biyar, inda aka ƙi basu, sai da safiyar yau Asabar ranar Zaɓe malaman zaɓe sunyi nufin Isa yankin sai saƙo yazo masu cewa, Ɓarayin sun hana, kuma sunce sai ambasu Miliyan Biyar a maimakon saɓa masu alƙawari da akai.
A ƙarshe dai malaman zaɓe basu iya isa wajen ba.
Banda wannan yanki, ko ina anyi Lafiya sai ɗan tsogwami da rashin fahimta da aka samu Can da in, wanda kuma basu tsaida zaɓen ba komi yatafi yanda Yakamata.