Kwamandan Operation Hadin Kai a Arewa-maso-Gabas, Christopher Musa, ya ce sama da ƴan ta’adda 79,000 da suka hada da mayaƙa da waɗanda ba mayaƙan ba ne suka mika wuya.
Musa, mai muƙamin Manjo -Janar ne ya bayyana haka a Maiduguri yayin da ya ke yi wa manema labarai karin haske kan nasarorin da rundunar ta samu a kwanakin nan.
Kwamandan ya ce ci gaba da kai hare-haren da ake kai wa ƴan tada kayar baya su ka miƙa wuya.
A cewarsa, hakan ya sa a ka buƙaci a samu ƙarin sansanoni a Maiduguri domin karɓar tubabbun da aka ware domin tantance maharan da wadanda ba mayakan ba.
Ya yaba da goyon bayan da jama’a ke ba su, wanda ya bayyana a matsayin “jarumai ” ya kuma bukace su da su ci gaba da dagewa wajen ganin an kawo ƙarshen rikicin cikin gaggawa.
Muna matukar farin ciki da yadda jama’a ke ba mu haɗin kai; suna ganin ikhlasi a cikin abin da muke yi.
Mun himmatu wajen bin ka’idojin kare hakkin dan Adam da ka’idojin tafiyar da ayyukanmu,” in ji Musa.