Yadda Aka Kaddamar Da Fom Din Da Kungiyoyin PDP Suka Siyawa Majigiri.

A ranar Asabar din nan 2 ga Afrelun 2022, gamayyar kungiyoyin jam’iyyar adawa ta PDP suka shirya taron hannatawa dan takarar gwamnan jihar Katsina karkashin inuwar jam’iyyar PDP, kuma shugaban jam’iyyar ta PDP a jihar Katsina,   Honorabul Salisu Yusuf Majigiri Fom din da suka sai masa, na takarar gwamnan jihar.

Taron kaddamar da Fom din dai, an yi shi ne a ofishin kaddamar da yakin neman za6en jam’iyyar ta PDP na karamar hukumar Mashi, taron da ya samu halartar masu ruwa da tsaki a matakin kananan hukumomi da kuma na jiha tare da rakiyar magoya baya.

A lokacin da yake kar6ar fom din, Majigiri ya nuna godiyarsa gami da jin dadi, tare da jinjina ga wadannan gamayyar kungiyoyi wadanda suka yi ruwa da tsaki wajen samar masa da fom din takarar.

A lokacin taron dai, Kungiyoyin jam’iyyar, Makada, ‘yan wasan kwaikwayo gami da magoya bayan jam’iyyar duk sun sami halarta.

Hakzalika, shugabanni da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun hada; Tsohon dan majalissar wakilan tarayya na jihar katsina kuma dan takarar sanata na jiha a karkashin jam’iyyar, Hamisu Gambo Dan Lawal, da kuma tsohon mataimakin dan takarar gamnan jihar katsina Rabi’u Gambo Bakori.

Sauran mahalartan sun hada da tsaffin ciyayomin kanan hukumomi, ‘yan majalissun tarayya da na jiha, da sauran daukacin magoya bayan jam’iyyar ta PDP.

Daga bisani bayan kammala taron, Majigiri ya kuma yi fira da ‘yan jaridu dangane da abin da ya shafi siyen fom din da kuma takararsa, da sauran wasu muhimman batutuwa da suka danganci takararsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here