Wani abun al’ajabi da mamaki ya faru a garin Kafur cikin ƙaramar hukumar Kafur din jihar Katsina inda muka samu labarin cewa an yi kuskuren binne wata yarinya da ran ta.

Majiyar mu ta Katsina Post ta bayyana cewar, yarinyar mai suna Sa’adatu Hassan Kafur dai ta yi doguwar suma ne sakamakon wutar lantarkin da ta taɓa wanda har aka yi tunanin ta rasu.

Wani ɗan garin wanda ya buƙaci mu sakaya sunan sa ya shaida mana cewa bayan doguwar suman da yarinyar tayi iyayen ta sun kai ta wani asibiti mai zaman kansa a garin Kafur ɗin inda ma’aikacin lafiyar da aka tarar ya faɗa masu cewar ta rasu.

“Da abun ya faru iyayen ta sun kai ta wani asibiti nan garin, amma likitan sai ya ce ta rasu. Daga nan ne ma suka maido ta gida aka yi mata wanka aka yi mata sutura. Amma da yake dare yayi, iyayen na ta suka sanya jana’izarta idan gari ya waye.” In ji shi

Majiyar ta mu ta kara da cewa da safiya ta yi kuma jama’a suka taru aka yi mata Sallah aka kuma kai ta maƙabarta aka binne ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Majiyar mu ta kara da cewa bayan an binne yarinyar wadda ke aji biyar (5) a makarantar Sakandare, sai labari ya riƙa yawo a cikin gari da kuma tsakanin makusantan ta na shakku da kuma tababar mutuwar ta ta.

Wasu daga cikin mutanen da suka ɗauki gawar a makara ne suka fara bayyana cewa sun ji kamar cikin yarinyar yayi kuka kuma ta yi tusa, amma dai gudun jawo ruɗani da cece kuce, sai suka yi shiru.

Haka zalika ma cikin ƴan uwan yarinyar da suka kwana da ita sun bayyana cewa sun ji motsi a cikin makarar amma sai suka yi tunanin ko bera ne a cikin ɗakin.

Daga ƙarshe dai aka dunguma zuwa maƙabartar aka tone ramin sannan kuma aka fito da ita da ran ta.

Bayan an fito da yarinyar da ran ta, iyayenta sun garzaya da ita zuwa asibin garin Malumfashi domin ceto rayuwar ta.

Sai dai labarin da muke samu yanzu shine bayan ƙokarin da aka yi na ceto rayuwar yarinyar, ta rasu kuma har ma an yi jana’izar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here