Gwamna Aminu Bello Masari na ci gaba da tuntuba da kuma tattaunawa da jakadun kasashen waje domin samar wa gwamnatin jiha da kuma ‘yan kasuwa abokan hulda domin habaka sana’o’i da kuma tattalin arziki.

Kan haka ne, ya karbi bakuncin Jakada Hidayet Bayrakhat na Kasar Turkiyya a Najeriya, wanda ya kawo mashi ziyara a masaukin Gwamna dake Abuja.

Da yake ma jakadan jawabi, Gwamna Aminu Masari ya shaida mashi cewa Katsina jiha ce ta noma, kiwo da kuma kasuwanci. Saboda haka muke bukatar ofishin jakadanci da yasa baki wajen kara zaburar da masu zuba jari daga kasar su shigo jihar Katsina domin hada guiwa da ‘yan kasuwar mu da kuma gwamnati wajen kafa cibiyoyin kasuwanci a jihar.

Gwamnan ya kuma bayyana wa jakadan cewa Gwamnatin Jiha tana bukatar taimako da kuma hada ka da kasar ta Turkiyya domin samar da horo kan hanyoyin kasuwanci na sana’o’i, noma da kuma kiwon lafiya.

Gwamnan ya kara da cewa samar da wannan horo zai canza rayuwar matasa wanda kuma sune kashin bayan al’ummar saboda dumbin yawan da suke dashi.

Alhaji Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa gwamnati za ta mika wadannan bukatun nata a rubuce ga ofishin jakadancin kasar Turkiyyar domin daukar matakin da ya kamata.

A nashi jawabin, Jakada Bayrakhat ya sha alwashin hada jami’an Gwamnatin Jiha da kungiyoyi da kamfanoni na kasar Turkiyyar wanda suke da tsari da zai yi daidai da bukatun da Gwamnatin Jihar ta gabatar.

Jakadan ya bayyana cewa akwai taro da suka shirya musamman kasashen Afirika wanda zai gudana a watan Disambar wannan shekarar wanda shi ne zai bada damar da ake bukata domin tattaunawa kan huldar kasuwanci da kuma bada horo kan hakan.

Mista Hidayet ya bayyana cewa kamfanonin Kasar Turkiyya sun nuna sha’awar su ta kara zuba jari a wannan kasa tamu mai tarin albarkatu da kuma yin hada ka da gwamnatocin jihohin Kasar nan. Wanda a yanzu haka akwai kamfanoni a jihohin Jigawa da Adamawa suna ci gaba huldatayyar su kasuwanci da zuba jari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here